Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugaban matatar mai ta Dangote, Alhaji Aliko Dangote da kuma kwamitin da ke aiki kan sayar da ɗanyen man fetur da Naira.

Shugaba Tinubu yayi ganawar ne a yau Talata a fadarsa da ke Abuja.
Ministan Kudi Wale Edun ne dai ya jagoranci kwamitin man fetur a yayin tattaunawar.

Sauran wadanda suka halarta taron sun hada da Alhaji Aliko Dangote, Shugaban Kamfanin Mai na Ƙasa NNPCL Malam Mele Kyari, Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Kasa FIRS Zacch Adedeji, da kuma Gwamnan Babban Bankin Kasa na CBN Yemi Cardoso da dai sauransu.

Bayan kammala ganawar ministan Kudi Wale Edun ya shaidawa manema labarai cewa sun tattauna ne akan shirin sayar da ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida a farashin kudin Kasar.
Ya ce shirin na shugaba Tinubu ya samu sakamakon zuba jari mai yawa da Dangote ya yi a matatarsa.
Edun ya ƙara da cewa dukkanin masu ruwa da tsaki sun ɗauki alƙawarin ganin shirin ya samu nasara tare da magance duk wata matsala da ka iya tasowa a cikin shirin.