Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi fatali da bukatar majalisar tattalin arzikin Kasar, na neman ya janye aniyarsa ta kasa kudin haraji a Kasar.

A yayin taron majalisar tattalin arzikin a jiya Alhamis ta bukaci shugaban ya janye batun karin haraji a Kasar.
Kafin zaman Majalisar na Jiya itama kungiyar gwamnonin arewa sun bukaci da shugaban ya janye kudurin nasa, inda suka bayyana cewa aniyar Tinubu ta saba da muradan yankin.

Majlisar ta ce ajiye batun karin harajin a gefe, hakan ne zai bayar da damar jin ta bakin masu ruwa da tsaki akan lamarin.

Sai dai bayan kirar da Majalisar tattalin arzkin ta yi Mai magana da yawun shugaban na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, ya ce shugaban Tinubu ya bukaci da majalisar ta Tattalin arziki da ta bari gwamnatinsa ta tabbar da sabuwar dokar kara haraji a fadin Kasar.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban ya ce ba zai janye kudurin ba daga gaban majalisar dokokin Kasar ba duk da sukar da ake yi masa akai.
Tinubu ya ce bai kara harajin ba sai da ya kafa wani kwamiti na tsawon shekara guda, inda ya ji ra’ayoyi game da kudurin daga bakin masu ruwa da tsaki akan tattalin arziki daga dukkan bangarorin kasar.