Wasu yan bindiga sun hallaka hugaban kungiyar Miyetti Allah a jihar Katsina.

Sannan sun tafi da matansa dayarsa.
An hallaka Alhaji Amadu Surajo da wasu mutane uku sannan su ka jikkata wasu da dama.

Lamarin ya faru a daren jiya Asabar wayewar yau Lahadi yayin da yan bindigan su ka kai hari kauyen Mai Rana da ke ƙaramar hukumar Kusada a jihar.

Bayan hallakashi sun sace matansa biyu da yarsa guda daya
Rahotanni sun ce za a yi jana’izar sa ne a yau Lahadi.
Tuni waɗanda aka jikkata aka kai su asibiti domin samun kulawa daga jami’an lafiya.
Zuwa yanzu yan sanda ba su ce komai dangane da harin da aka kai ba.