Jam’iyyar PDP a Najeriya ta ce a zaɓen da za a yi na shekarar 2027 za ta lashe ƙarin kujerun gwamna a ƙasar.

Kwamitin gudanarwar na jam’iyyar ne su ka bayyana yaka a yau Lahadi yayin da su ka ziyarci gwamnan jihar Bayelsa Dauye Diri a gidansa.

Ma’ajin jam’iyyar na ƙasa Alhaji Ahmed Yayare ne ya bayyana haka ya ce sakamakon halin da ake ciki na matsin rayuwa zai basu damar lashe karin kujerun gwamna a zabe na gaba.

A cewarsa, jam’iyyar PDP ita kaɗai ce jam’iyyar da za ta iya karbe mulki daga jam’iyya mai mulki ta APC.

Ya kara da cewa mutane na kokawa a kan yunwa da wahalhalu da ake ciki wanda hakan zai basu dama ta samun nasara a shekarar 2027.

Kwamitin sun kai ziyarar jajantanwa gwamna Diri ne bisa mutuwar tsohon sufeton yan sanda na kasa Mosed Jituboh da kuma kwamishinan al’amuran mata a jihar.

A cewarsa, zuwa yanzu jami’yar PDP ta zage damtse tare da daura damba don shiga zaben da kuma yaƙinin samun nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: