Wata motar dakon mai da ta fashe ta yi silar mutuwar mutane da dama yayin da gidaje su ka kone a jihar Delta.

Lamarin ya faru a jiya Lahadi a Agbor hanyar tsakanin Legas zuwa Asaba da ke ƙaramar hukumar Ika ta Kudu a jihar.


Shaidu sun ce faduwar motar ya haifar da cunkoso a yankin
Gidaje daa dama ne su ka ƙone yayin da wasu mutane su la rasa rayukansu.
Wani mai suna Chuks Ogwude da lamarin ya faru a gabansa ya ce wutar ta bazu ko’ina cikin kankanin lokaci sai dai sun yi iya bakin kokarinsu.
Sakamakon jinkiri da aka samu kafin kai dauki ne ma ya sa mutanen yankin su ka nuna rashin jin dadinsu.
Daga bisani jami’an yan sanda da na hukumar kashe gobara a jihar sun isa wajen domin bayar da agajin gaggawa.
Gwamnan jihar ya mika sakon taaziyyqrsq ga wadanda lamarin ya shafa.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Sir Festus Ahon ya ce lamarin ya girgizashi sosai saboda girmansa.
Sannan ya sha alwashin tallafawa iyalan wadanda ibtilain yaa abkawa