Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar Ghana domin shaida rantsar da sabon shugaban kasar John Dramani Mahama.

 

Hakan na kunshe a wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar a daren jiya.

 

Sanarwar ta ce shugaban zai tafi ƙasar Ghana a yau Litinin, haakan ya biyo bayna gayyatar da aka aikewa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

 

A watan Disamba na shekarar da ta gabata shugaba Tinubu ya gana da zababben shugaban kasar Ghana Jorhn Mahama a Abuja.

 

Shugaba Tinubu zai halarci taron ranstuwar a matsayin shugaban kungiyar Ecowas kuma shugaban Najeriya.

 

Tun bayan zaban da aka sanar da nasarar Mahama, Tinubu ya bayyana hakan a matsayin wata nasara ga Ecowas ganin irin ci gaba da ake sa ran samu sakamakon hadin kai da shugaban zai bayar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: