Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kori jami’an ta 27 bayan samunsu da laifin damfara da wasu laifuka da su ka saba da ƙa’idar aikin.

 

Shugaban hukumar Ola Olukoyede ya ce hukumar ta ɗauki matakin haka ne domin yaƙi da rashawa tare da gargadin jami’an don ganin sun shiga taitayinsu.

 

A cewarsa sun dauki matakin ladaftarwa ga jami’an tare da nuna musu cewar ba za su lamunci rashin daa na.

 

Ola wanda mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya yi magana a madadinsa, ya ce hukumar ta himmatu wajen yakar rashawa a cikinta.

 

Haka kuma su na tabbatar da cewar sun yi bincike kan duk wani jami’i da ake zargi da hannu a kan wata badaƙala da ta kuɗi da ake zargi a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: