Helkwatar tsaro a Najeriya ta tabbatar da kisan jami’an soji shida a wani hari da mayakan Iswap su ka kai wa jami’an a sansaninsu a jihar Borno.

An kai harin ne a Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Daboa a jihar ranar 4 ga watan Janairu da mu ke ciki.
Mai magana da yawun helkwatar Edward Buba ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yau

Ya ce sun mayar da martani inda su ka hallaka mayakan su 34.

Jami’an sun kuma kwato bindigu kirar AK47 guda 23 da wasu makamai.
A cewarsa, an kai wa mayakan Iswap din harin ne ta sama.
Da farko mayakan sun dirarwa jami’an yayin da su ka je dauke da muggan makamai haye kan babura.
Sanarwar ta ce an kai wa sojin harin ne bayan hallaka wani babban kwamandan ƙungiyar.