Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano Yusuf Imam wanda aka fi sani da Ogan Boye, ya nada mutane 60 a matsayin masu taimaka masa akan ayyukan ƙaramar hukumar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar amincewa mai dauke da sa hannun Sakataran karamar Hukumar Ado Muhd Hotoro.
Sanarwar ta ce shugaban karamar hukumar hukumar ya amince da nadin mutanen, a kokarin da yake yi na ciyar da karamar hukumar gaba.
Hotoro ya ce an nada mutanen ne a mukamai daban-daban don ganin sun taffawa shugaban karamar hukumar a yunkurinsa na inganta karamar hukumar tasa.
A cewar Sakataren mutane 18 daga cikin wadanda aka nada za su yi aiki ne a bangaren dauko rahotanni na musamman don yin duba akan bangariri daban-daban, kasuwanni, da kuma cibiyoyin kula da lafiya na Ƙaramar Hukumar ta Nasarawa.
Sauran sun hada da Mataimaki na Musamman, shugaban Tsare-Tsare, Shugabannin Harkokin Bayanai, Sakataren Ma’aikatan Ƙaramar Hukumar, da kuma Shugabannin Daraktoci guda takwas.
Sannan takartar nadin ta ce an nada mutanen ne bsakamakon cancantarsu, gaskiya, da kuma jajircewa.
A karshe kuma Shugaban Karamar Hukumar ya yi musu fatan samun nasara a gudanar da ayyukansu, tare da yin kira agaresu da su gudanar da ayyukan da aka nada kowanne su yadda ya kamata domin ganin karamar hukumar ta ci gaba.


