Gwamnatin ƙasar Faransa ta musanta zargin da jagororin ƙasar Nijar su ka yi kan cewar su na haɗa kai da Najeriya domi yi wa Nijar zagon ƙasa.

Mai ba da shawara kan siyasa na ofishin jakadancin Faransa a Najeriya Mista Bertrand de Siessan ne ya byyana haka yayin wata ganawa da aka yi da shi a Abuja.


Ya ce zargin da shugaban soji na Nijar ya yi babu ƙamshin gaskiya a cikinsa sannan ba a taɓa tattauna makamancin haka a kai ba.
Idan za a iya tunawa shugaban soji na Nijar Abdourahamade Tchiani ya zargi Najeriya da hada kai da Faransa don yin amfani da iyakokin ƙasar tare da yi musu zagon ƙasa.
Lamarin da ya haifar da cece ku ce kuma daga bisani gwamnatin Najeriya ta musanta.
Itama ƙasar Faransa ta musanta batun wana ta ce ba ta da wani shiri na hada kai da Najeriya domin cutar da Nijar.