Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci da a gaggauta yin bincike kan harin da mayaƙan ISWAP su ka kai wa jami’an soji a jihar Borno.

 

Tinubu ya jajanta kan lamarin tare da buƙatar gaggauta tono yadda aka kitsa harin da waɗanda su ka kai.

 

An kai wa sojon hari ne a ranar 4 ga watan Janairu a sansaninsu da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa a jihar

 

Sojo shida ne su ka rasa rayukansu yayin da mayakan su ka cinna wuta a sansanin da kuma motocin jami’an.

 

A wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu Bayo Onanuga ya fitar kan batun, Tinubu ya nuna damuwa da kuma takaici kan yadda aka halaka sojin.

 

Rahotanni sun ce bayan an kai wa sojin hari, jami’an sojin sama sun mayar da martani a wani hari da su ka kai ta sama tare da halaka mayaka sama da 30.

 

Helkwatar tsaro ta ce an kai wa sojon harin ne bayan da sojin su ka hallaka wani kwamandan kungiyar

Leave a Reply

%d bloggers like this: