Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta batun hallaka farar hula a jihar Zamfara.

Ana zargin jami’an sun hallaka yan sa kai 16 yayin da wasu su ka jikkata a wani hari da su ka kai ranar Asabar.


An kai harin ne kauyen Tungar Kara da ke karamar hukumar Maradun a jihar
Sai dai jami’an sojin saman sun musanta batun hallaka yan sa kai ɗin.
Mai magana da yawun sojin saman Najeriya AVM Akinboyewa ya ce su na ɗaukar matakaan da ya kamata domin kare fararen hula a hare-haren da su ke kaiwa.
Ya ce batun da ake yadawa cewar an hallaka farar hula a jihar farfaganda ce da yan bindiga ke yaɗawa domin hana jami’an ci gaba da gudanar da ayyukansu.
Ya ce babu wata kwakkwarar hujja da ke nuna cewar an haallaka mutanen.
A cewarsa, an fara gudanar da bincike kuma za a fitar da hakikanin abin da ya faru bayan kammala bincike.
Ya ce harin da su ka kai Tungar Kara sun hallaka yan ta’adda ne sannan su ka kubutar da mutane da aka yi garkuwa da su.
Tun a jiya Lahadi aka yi jana’izar mutane 16 yan sa kai da aka hallaka yayin da su ke shiri don tunkarar yan bindiga.
Gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ya mika sakon taaziyyarsa ga iyalan waɗanda aka hallaka.