Hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya ta ce fiye da mutane 48,932 ne ke jiran hukuncin a gidajen da ke faɗin ƙasar.

 

Mai riƙon mukamin shugabancin hukumar ta ƙasa Sylvester Nwakuche ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin.

 

Ya ce hukumar na fuskantar kalubale na cunkoson mutane a gidajen ajiya da gyaran hali

 

Sai dai ya ce za su hada kai da hukumar shari’a ta ƙasa, da babban sufeton yan sanda da kuma sauran hukumomin tsaro da ke gurfanar da masu laifi a gaban kotu don duba hanyar da ka iya zama mafita.

 

Sannan ya buƙaci manyan jami’an musamman wadanda ke jihohi da su haɗa kai da alkalan jihohin don ganin an gaggauta yanke hukunci ga waɗanda ake tsare da su.

 

Ya ce a yanzu babu wani abu da ke ci wa hukumar tuwo a kwarya kamar cunkoson da ake da shi a gidajen da ke Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: