Babagana Zulum

Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da kisan mutane sama da 40 da ake zargi mayakan ƙungiyar Boko Haram sun yi.

 

Mayakan sun hallaka manoman ne a wani hari da su ka kai a yammacin jiya Lahadi.

 

Da yake tabbatar da lamarin, Kwamishinan yaɗa labarai a jihar Farfesa Usman Tar ya ce harin da aka kai ta’addanci ne.

 

Sannan gwamnan jihar Babagana Zulum ya yi Ala Wadai da harin.

 

Gwamnatin ta ce za ta tabatar ta gudanar da bincike a kan lamarin tare da kokarin daukar matakin da ya dace

 

Fiye da mutane 40 aka hallaka yayin da wasu da dama ba a gansu ba.

 

An kai harin a yammancin jiya Lahadi a kusa da Baga da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: