Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a kammala aikin titin Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja cikin watanni 14 masu zuwa.

 

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin kaddamar da sashe na farko na aikin.

 

Sashe na farko na aikin da aka kaddamar shi ne daga Kaduna zuwa Abuja yayin da kaso na biyu ya kama daga Kaduna zuwa Zaria sai kuma kaso na uku daga Zaria zuwa Kano.

 

A cewar ministan, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya himmatu matuka wajen ganin aikin ya kammala cikin watanni 14 kamar yadda su ka sha alwashi.

 

Ya ce shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da dukkan umarnin kuma majalisar dattawa ta bayar da hadin kai a don haka babu abinda ya rage sai ci gaba da aikin.

 

Ministan ayyuka a Najeriya David Umahi ya ce kara tsawaita aikin da ƙarin kilo mita biyar daga Kano zuwa babban filin sauka da tashin jirage sama na kasa da ƙasa a jihar Aminu Kano International Airport.

 

Sannan akwai ƙarin tsawaita aikin da aka yi daga Abuja zuwa ƙarshen babbar hanyar zuwa Lokoja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: