Wata gagarumar girgizar ƙasa ta afku a yankin kudancin ƙasar Taiwan da safiyar yau Talata, inda ta jikkata aƙalla mutane 27 da kuma rushe manyan gine-gine da tituna kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Girgizar ƙasar ta afku ne da misalin ƙarfe 12:17 na wayewar garin yau Talata, inda tsayin ta ya kai kilomita 9.7 a yankin Chiayi, mai tazarar aƙalla kilomita 200 zuwa kudancin Taipei.

Wata mata da aka tseratar da ita daga cikin gini mai hawa shida, a zantawarta da gidan talabijin na Taiwan ta bayyana cewa, lokacin da ta ji ƙarar afkuwar girgizar ƙasar, sai da ta gigita tare da faɗowa daga kan gado.

Daga ɓangaren masu aikin bayar da agajin gaggawa sun bayyana cewa, gine-gine da dama sun ruguzo tare da wasu mutanen a ciki, kafin daga bisani a ceto su.

Inda kuma suka ruwaito cewa, tituna da wasu gine-ginen ababen more rayuwa duk sun salwanta, da kuma samun katsewar wutar lantarki a yankin kudancin birnin Kaohsiung.

Shugaban yankin Cho Jung-tai ya ziyarci wuraren da iftila’in ya shafa a Tainan yau Talata, inda ya jajantawa mazauna yankin da aka kuɓutar daga gine-ginen da suka rushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: