Ƙungiyar jam’iyyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta sake aikewa da gwamnan Jihar Filato Caleb Muftwang Bukatar komawa jam’iyya mai mulki ta APC.

A wata sanarwa da shugaban kungiyar Saleh Zazzaga ya fitar a yau Asabar a Abuja, inda ya bukaci da gwamnan na Filato da ya koma jam’iyyar ta APC kafin ranar taron jam’iyyar da ke tafe.
Kungiyar ta ce komawar Caleb cikin jam’iyyar ta APC hakan zai kara bashi damar samun damarmaki don kara kawowa Jiharsa ci gaba, da kuma ba shi damar zama jagoran jam’iyyar a Jihar ta Filato.

Ƙungiyar ta ce a yankin Arewa ta Tsakiya Jihar Filato ce kadai ba a karkashin mulkin jam’iyyar APC ba, inda ya ce shiga jam’iyyar ta.

Har ila yau kungiyar ta ce matukar Caleb bai koma jam’iyyar APC zai iya rasa kujerarsa a yayin zaben shekarar 2027 mai zuwa, sakamakon rikicin da jam’iyyar ta PDP ke fama dashi.
Kungiyar ta ce ta yanke shawarar mika bukata ga gwamna Caleb ne sakamakon irin nasarorin da ya ke samu akan kujerar gwamnan Jihar tare da kudurin jam’iyyar na kara karfafa hadin kai.
Acewar Zazzaga komawa APC daga PDP hakan zai sanya gwamnan ya kara samun damar aiki kafada da kafada da Shugaba Tinubu domin cimma muradin ci gaban al’umma Jiharsa.
Idan ba a manta ba a watan Afirilun shekarar 2024 da ta gabata, kungiyar ta aike da wasikar gayyata ga gwamnan na Filato, bayan da kotun koli ta tabbatar da nasararsa ta zama gwamnan Jihar.