A gobe Lahadi ne shugaban Kasa Bola Tinubu zai bar birnin tarayya Abuja zuwa birnin Dares Salaam na Kasar Tanzaniya, don halartar taron shugabannin Afirka kan makamashi.

Mai magana da yawun shugaba Tinubu kan yada labarai Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Sanarwar ta Onanuga ta bayyana cewa Gwamnatin Kasar Tanzania tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Raya Afirka da Bankin Duniya ne za suka nauyin taron,

Onanuga ya kara da cewa taron zai mayar da hankali ne akan bunkasa shirin nan na ‘Mission 300’ domin samawa mutane miliyan 300 wutar lantarki a yankin Afirka zuwa shekarar 2030 mai zuwa.

Bayo ya ce a yayin taron shugabannin yankin Afirka da shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, da kuma kungiyoyin fararen hula za su halarci taro, inda kuma za su tattauna akan kara samar da dabarun samun wutar lantarki a nahiyar ta Afrika, sannan kuma zai mayar da hankali akan samar da wutar lantarkin a yankunan karkara, da sabunta manufofin makamashin, da amfani makamashi mai inganci, da kuma jawo kamfanoni masu zaman kansu domin zuba hannun jari a ciki.

Acewar sanarwar a rana ta farko Najeriya da sauran Kasashen da za su halarta taron za su gabatar da jawabi akan dabarun samar da wuta ga ’yan Kasarsu a cikin shekaru biyar.

Sannan kuma a rana ta biyu shugabannin Kasashen za su sanya hannu akan yarjejeniyar makamashi ta Tanzaniya wadda za kuma ta bayyana hanyar da za a bi wajen cimma bunkasar shirin.

 

Onanuga ya ce Shugaba Tinubu zai yi jawabi domin tabbatar da kudurin Najeriya na samar da wutar lantarki ga ‘yan Kasar da kuma himmar da take yi wajen ci gaban makamashi a yankin na Afirka.

Za dai a gudanar da taron ne a ranakun 27 da 28 ga Janairu nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: