Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da tsawaita wa’adin sabunta rajistar gidaje da filayr a Jihar.

Mukaddashin babban sakataren ma’aikatar Kasa da tsare-tsare Muhammed Musbahu Yahuza ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
Sanarwar ta ce ta kara wa’adin yin rajistar ne, bayan amsa rokon al’umma na kara wa’adin, wanda ya kare a yau juma’a.

Sanarwar ta ce an tsawaita wa’adin ne zuwa ranar 1 ga watan Afrilun shekarar nan da muke ciki.

Sanarwar ta kuma bukaci dukkan masu gidaje da filaye da su ta tabbata da sun sabunta rajistar su domin tun kafin lokacin daukar matakin doka.