Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ta hallaka yan bindiga 358 yayin da ta kama 431 cikin watan Janairun da mu ke ciki.

Mai magana da yawun helkwatar Edward Buba ne ya bayyana haka wanda yace sun kubutar da mutane 249 cikin watan.
Haka zalika sun kwato danyen mai da aka sata da ya kai darajar naira miliyan dubu biyu da milyan 699,660,460.

Sannan akwai makamai 370 da harsashi guda 4972 da su ka kwato.

An kubutar da lita 2,732,038 na danyen mai tare da kwato tataccen man fetur da kalanzir da sauran dangogin sinadaran danyen mai.
Buba ya sake jaddada cewar za su ci gaba da yaki da ta’addanci a Najeriya.