Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta tabbatar da kama wani mafarauci mai suna Yusuf Garba mai shekara 55, wanda ake kira da Gana bisa zarginsa da hako kabarin wani mutum tare da yanke masa kai.

Mai magana da yawun da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar SP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar da kama wanda ake zargi.
Nguroje ya bayyana cewa wanda ake zargin an same shi ne da yanke kan mijin mahaifiyarsa, bayan ya tono gawarsa, inda wanda ake zargin ya amsa laifinsa yayin da ake masa tambayoyi.

Acewar Kakakin rundunar, mai laifin dan asalin garin Tappare Kona Uku ne da ke karamar hukumar Jada ta jihar, ya ce wanda ake zargin ya shaida musu cewa dan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan ya mutu.

Wanda ake zargin ya kara da cewa shekara daya bayan mutuwar mijin mahaifiyartasa, dan mijin na mahaifiyar tasa ya matsa masa lamba akan yanko kan, inda ya tabbatar da cewa shi din matsafi ne da ka iya cutar da shi ko ‘ya’yansa matukar yaki cika umarninsa.