Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta dauki tsauraran matakai domin tabbatar da tsaro da kare rayukan Al’ummar jihar Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar CP Salma Dogo Garba ne ya tabbatar da hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar hukumar da ke Bampai a Kano a yau Juma’a.
Kwamishin ya ce idan ba za’a manta ba rundunar ‘yan sandan ta bayar da sanarwa ga Al’ummar Jihar, da su sanar da ita dukkan motsin wani mutum ko wani abu da aka gani ko aka ji wanda ba a yadda dashi ba ga jami’an rundunar.

Hakan dai ya biyo bayan wani rahoto da aka samu daga jami’an rundunar bisa wasu ababan fashewa da suka gano a Jihar.

Acewar CP Salman Dogo wani mai suna Ahmad Adam Abba dan kasar Chadi wanda ake zargi da jagorancin kisan mutane 17 a kasar Chadi an kama shi a yayin da yake kokarin samun guri domin aikata ta’addanci a nan Kano.
Sai dai wanda ake zargi dan kasar ta Chadi ya tsere daga nan Najeriya, inda aka kama mutane uku da ake zargi suna tare cikinsu harda matarsa wanda aka kaman mai suna Jibrin Muhammad dan shekara arba’in da haihuwa da kuma wani dan Najeriya.
CP Dogo ya shaidawa manema labarai cewa rundunar na ci gaba da kokari dan ganin babu wata mafaka ga masu aikata laifi ko niyyar aikata laifi a jihar kano, inda ya ce jami’nsa sun hada kai da sauran jami’an tsaro da al’ummar Jihar domin yin aiki kafada da kafada don gano batagari a dukkan inda suke a fadin Jihar.
A karshe ya bayyana cewa jami’an rundunar na kewayawa dukkan lungu da sako na jihar ta kano, inda ya ce sashin hulda da jama’a na rundunar zai cigaba da wayar da kan al’ummah bisa muhimmancin sanar da rundunar abinda aka gani ko aka ji ba’a yarda dashi ba.