Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Abba Abubakar Aliyu a matsayin shugaban hukumar wutar lantarki ta karkara REA.

Mai magana da yawun shugaban kan yada labarai Bayo Onanuga ne ya tabbatar da nadin ta cikin wata sanarwa wadda Olusegun Bada hadimin shugaban na musamman ya fitar a yau Juma’a.

Sanarwar ta ce sabon shugaban hukumar ta REA zai shafe tsawon shekaru hudu akan mukamin, inda kuma nadinnasa ya fara aiki tun daga ranar 23 ga Janairun shekarar nan.

Kafin wannan nadin Abba ya kasancewa mukaddashin shugaban hukumar ta REA tun a watan Maris din shekarar 2024 da ta gabata har zuwa nadin da shugaba Tinubu yayi masa.

Bayo ya bayyana cewa Abba Aliyu nada kwarewar shekaru 20 a fannin makamashi da kuma ci gaban hukumar.

Onanuga ya ce ya kuma bayar da gudunmawa a bangarorin wutar lantarki a Najeriya da adana albarkatun ruwa da na bangaran zirga-zirga wanda hakan ya bunkasa tattalina rzikin Najeriya.

Sannan ya kara da cewa kafin nadin Abba Aliyu shi ne shugaban sashen kula da ayyuka na shirin samar da wutar lantarkin a Kasar, kuma babban Manajan ayyukan na hukumar, sannan mataimakin shugaban kamfanin NBET.

Acewar Sanarwar shugaba Tinubu na fatan sabon shugaban hukumar zai yi amfani da kwarewarsa wajen kara daga Likafar hukumar don samun nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: