Jami’an soji hudu ne su ka rasa rayukansu yayin da wasu ke asibiti ana kula da su bayan da wata mota ta bi ta kansu.

Ana zargin direban motar na cikin mayen giya lamarin da ya kai ga ya bi ta kan sojojin.

Al’amarin ya faru ajihar Legas yayin da sojin ke motsa jiki a safiyar yau Juma’a.

Jami’an sojin na aiki ne a barikin Myoung da ke Morocco a yankin Shomolu.

Bayan faruwar lamarin direban ya nufi tserewa sai dai mutane sun kamashi.

Faruwar hatsarin ya haifar da cunkoso da hayaniya a wajen.

Zuwa yanzu mahukunta ba su ce komai a kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: