Bankin duniya ya sanar da cewa, ya ware Dala biliyan 1.2, don haɓaka ilimin yara mata a jihohi 18 na faɗin Najeriya.

Jihohin da za su ci gajiyar shirin sun haɗar da; Borno, Ekiti, Kebbi, Kaduna, Filato, Katsina, Kano, Adamawa, Kogi, Nasarawa, Neja, Bauchi, Jigawa, Yobe, Kwara, Gombe, Sokoto da kuma jihar Zamfara.

Babban daraktan bankin duniyar a Najeriya Ndiame Diop ne ya sanar da hakan, yayin ƙaddamar da shirin tallafawa ilimin yara mata da aka fi sani da AGILE, jiya Juma’a a birnin tarayya Abuja.

A jawabinsa Diop wanda ya samu wakilcin babban ƙwararren mai bayar da kariya ga al’umma Tina George ya ƙara da cewa, babban kuɗirin shirin shi ne samar da cikakken goyon baya don haɓaka ilimin yara mata a makarantun sakandire da kuma tallafa musu.

Ya kuma ce su na hanƙoron shigar da kimanin ɗalibai miliyan 15.2 cikin shirin, wanda ya ƙunshi yara mata miliyan 8.6 masu aure da marasa aure, da kuma masu buƙata ta musamman a jihohi 18 na faɗin ƙasar.

Ya kuma bayyana cewa zuwa yanzu shirin na AGILE ya gina makarantun sakandire kimanin guda 104, da kuma gyara waɗanda su ka lalace guda 3,922 duk don tallafawa ilimin yara mata da maza.

Leave a Reply

%d bloggers like this: