Gwamnatin Jihar Oyo ta sauya matsayin wasu ma’aikatan wucin gadi su 1,591, zuwa ma’aikatan dindindin na jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan al’umma na jihar Dotin Oyelade ne ya sanar da hakan, tare da cewa gwamnan jihar Seyi Makinde ya ɗauki wannan matakin ne tun a watan Oktoba na shekarar da ta gabata.

Ya kuma ƙara da cewa, gwamna Makinde ya amince da mayar da ma’aikatan wucin gadin zuwa matsayi na dindindin, a cibiyoyi 33 da ke jihar.

Dotun ya kuma bayyana cewa, an yi hakan ne dan cike gurbin ma’aikata a matakan ƙananan hukumomi, kuma an bi ƙa’idar aiki yayin tabbatar da sauyin.

Ya kuma ƙara da cewa, waɗanda su ka rabauta da samun aikin, za su karɓi takardunsu na kama aiki nan ba da daɗewa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: