Hukumar masu yi wa ƙasa hidima ta NYSC, ta yi kira ga mambobinta da su kaucewa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi don kare kansu daga illolinta.

Shugaban shirin na NYSC a jihar Ribas Moses Oleghe ne ya bayyana hakan, yayin gabatar da bita da wayar da kai ga masu yi wa ƙasa hidima a sansaninsu da ke Nowa Tai a jihar.
An gudanar da bitar ne dai a sansanin na su, bisa haɗin guiwa da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA.

Oleghe ya ƙara da cewa an ƙuduri aniyar aiwatar da shirin ne dai, don buƙatar haɗa hannu akan haƙi da miyagun ƙwayoyi.

Moses ya kuma bayyana irin illolin da ke tattare da shan miyagun ƙwayoyi a cikin al’umma, inda ya bukaci masu yi wa ƙasa hidimar da su kasance a gaba-gaba wajen yaƙi da shi maimakon zama ɗaya daga cikin masu yi.
