Jam’iyya mai mulki a Najeriya ta APC ta bayyana korar tsohon gwamnan jihar Osun, wato Rauf Aregbesola daga jam’iyyar.

Cikin wata wasika da aka fitar daga sashin jam’iyyar na jihar sun tabbatar da korar ta Aregbesola, sakamakon zarginsa da zagon ƙasa da munafuntar jam’iyyar.

 

Aregbesola wanda tsohon ministan harkokin cikin gida ne a gwamnatin da ta gabata, ya ƙirƙiro tsarin ƴan a ware a cikin jam’iyyar a jihar ta Osun, sakamakon rashin jituwa da ta ke tsakanin jagororin jam’iyyar.

Cikin wata wasika da aka fitar mai taken “zarge-zargen zagon ƙasa ga jam’iyya – hukuncin da shugabannin jam’iyya na jiha su ka ɗauka a kanka” an zargi Aregbesolan da karya sashi na 21 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, wanda ya bayyana hukuncin duk wanda ya aikata laifin.

Inda a ƙarshen wani ɓangaren na wasikar ya sanar da cewa, sun yanke shawarar korarsa daga jam’iyyar.

Korar ta tsohon gwamnan ta biyo bayan wani zaman ganawa da tsaginsa ya yi a ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka yanke shawarar fita daga jam’iyyar ta APC, sakamakon taɓarɓarewa da su ka ce jam’iyyar ta na yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: