Ƙungiyar ‘yan kasuwar man Fetur ta PETROAN ta bayyana cewa nan bada jimawa ba farashin man fetur zai fadi Kasa warwas, sakamakon farfaɗo da matatun man Port Harcourt da Warri a Kasar.

Mai magana da yawun kungiyar Dr Joseph Obele ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar.

Sanarwar ta bayyana cewa a halin yanzu matatun na gudanar aikin tace man sosai.

Acewar sanarwar matakin zai ci gaba da kawo sauye-sauye masu albanu ga tattalin arzikin Najeriya ,musamman wajen saukar farashin man fetur din.

Kakakin kungiyar ya kara da cewa dawowar aikin matatun Port Harcourt da Warri hakan ne zai kawo gasa a kasuwar man fetur, wanda kuma hakan zai sanya farashinsa ya dawo kasa warwas, wanda hakan kuma zai taimakawa ‘yan Kasar.

Sanarwar ta ce ‘yan kungiyar na sayan man a matatun, kuma hakan zai kawo karshen dogara da shigo da tataccen man daga kasashen Ketere, sannan zai taimaka wajen daidaita farashin canjin Dala.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa a baya kafin dawo da aikin matatun Kasar, man fetur din bogi yayi yawa a kasuwa, amma a halin yanzu man na bogi ya ragu a Kasuwanni.

Har ila yau PETROAN ta ce farfaɗo da matatun ya taimaka matuka wajen rage yawaitar satar danyen mai, wanda hakan ya hana Kasar cimma burinta na adana danyen mai.

Sannan sanarwar ta cewa aikin matatun zai taimaka wajen kara bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: