Rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta bayyana cewa, ta daƙile wani harin yin fashi da makami tare da cafke mutane uku da, ake zargi a cikin garin Bauchi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan a jihar ta Bauchi CSP Ahmed Wakili ne ya bayyana hakan, ga manema labarai jiya Juma’a a garin na Bauchi.
Ya kuma bayyana cewa sashin binciken ƙwaƙwaf da bin diddigi na rundunar ne su ka aiwatar da aikin, kuma waɗanda ake zargin sun ƙware ne ga tare masu hada-hadar kuɗi a bankuna, da suka fito daga jihohin Borno, Bauchi da kuma Kano.

Ya ce waɗanda ake zargin su na fakon mutane ne idan su ka cire kuɗi masu yawa daga banki, sai su bi bayansu su far musu da fashi da makami, inda a wannan karon su ka tasamma wani mutum ɗan kasuwa mai shekaru 43, wanda ya cire kuɗi daga bankin FCMB a Bauchi.

Waɗanda ake zargi dai tuni su ka amsa laifukansu, tare kuma da bayar da bayanin da zai taimaka wajen cafko babbansu.
Wakili ya ƙara da cewa, rundunar ta su sun samu nasarar karɓo wasu mabuɗan mukulli na musamman guda uku, da ƙananan motoci ƙirar Toyota Honda guda biyu, da kuma sauran wasu kayan shaidu.