Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane biyar a wani hari da suka kai kauyen Lighitlubang da ke yankin Bungha a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga kauyen ne a da misalin karfe 12:00 na daren jiya Juma’a, lokacin da mazauna yankin ke tsaka da bacci.

Daga cikin mutanen da maharan suka hallaka sun hada da wani mutum da matarsa da kuma ɗansu, da kuma wasu suma miji da matar.

Maharan sun hallaka mutanen ta hanyar yankasu da suka yi.
Wani mazaunin kauyen Moses Bankat ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai a yau Asabar.
Ya ce maharan sun shiga Kauyen ne ta yadda ba za a iya gane su ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ya Alabo Alfred ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni suka aike da jami’an tsaro yankin, kuma su na gudanar da bincike.