Gwamnatin tarayya ta musanta jita-jitar cewa za ta yi karin kaso 65 cikin 100 na kudin wutar lantarki a Kasar.

Mai bai’wa shugaba Tinubu Shawara kan Makamashi Olu Arowolo ne ta yi karin bayani akan batun karin kudin wutar a yau Litinin.
Sanarwar ta ce babu kamshin gaskiya a cikin batun, inda aka yi kuskure wajen fassara bayanan da aka fitar daga akan batun karin kudin wuta.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokarin wajen mayar da hankali akan inganta bangaren wutar lantarki don saukakawa al’ummar Kasar daga karin da za su gaza akansa.

Kazalika ya kara da cewa gwamnatin ta tarayya na cike gibin da ya yi saura , inda ta ke ci gaba da bayar da tallafin domin samu damar rarraba hasken lantarki ga al’umma.
Sanarwar ta bayyana cewa babu wata aniya ta karin kudin wutar lantarki ga ‘yan Kasar, inda kuma gwamnatin za ta bayar da tallafin da ya hada da sanya mita, tallafi na musamman, warware basussuka, da kuma samar da makamashi na zamani a Kasar.
