Gwamnatin Jihar Katsina Karkashin jagorancin gwamna Malam Umar Dikko Radda ta fitar da Naira miliyan 252 domin tallafawa matasa 1,016 a dukkan fadin Kananan hukumomin Jihar 34.

Hukumar Raya Kamfanoni ta Jihar ta Katsina KASEDA ke gudanar da shirin da wanda ke karkashin Shirin gina goben matasa da ci gabansu.
Hukumar ta gudanar da rabon tallafin ne a yau Talata a Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jihar.

Gwamnatin ta yi hakan ne domin ganin matasa sun tsaya da kafafunsu, don ganin sun zubar da makamansu daga aikata miyagun laifuka, da kuma kawo karshen yin maula a ma’aikatun gwamnati.

A yayin jawabin gwamna Radda a gurin taron ya bayyana cewa wannan guda ne daga cikin alkawurran da ya daukarwa al’ummar Jihar a lokacin yakin neman zabensa.
Gwamnatin Jihar na kuma fatan shirin ya sauya rayuwar matasan daga munanan dabi’u marasa kyau.
Daga cikin hukumomin da suka halarci taron sun hada da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kasa NDLEA, jami’an ‘yan sanda, hukumar Hisbah, shugabannin addini, sarakuna, da kuma sauran manyan jami’an gwamnatin Jihar.
