Mai bai’wa shugaban Kasa Tinubu shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya bukaci da Hajiya Naja’atu Muhammad da ta nemi ya fiyarsa akan wani bidiyo da ta yi a Kafar Tik Tok.

Ribadu na Neman Hajiya Naja’atu na janye kalaman ne bisa zarginsa da ta da gudanar da aiki a cikin gwamnatin shugaba Tinubu, duba cewa a baya a lokacin da yake shugabantar hukumar EFCC ta zargi shugaba Tinubu da wasu gwamnoni da aikata almundahana.
Naja’atu ta kuma ce a halin yanzu Ribadu ya zama wanda yake kare shugaba Tinubu, akan gwamnatisa don hana mutane sukar gwamnatin ta Tinubu.

Sai dai a cikin wata wasika da Lauyansa Dr Ahmad Raji ya fitar yau Talata, ya ce Naja’atu ta yi hakan ne da nufin batawa Ribadu suna.

Acewarsa ko kadan Ribadu bai taba fadin irin wadannan kalami ba ko a fili ko kuma a boye.
Rubadu ya bukaci da Hajiya Naja’atu da ta fado hujjoji akan kalamanta akanshi, duba da cewa bidiyon da ta babbar barazanace wanda ka iya haifar da rikici a yankin Arewa, wanda hakan ya sanya ba zai kyale kalaman nata ba.
Wasikar ta bukaci da Naja’atu da ta fito ta yi kalaman ban hakuri a jaridu guda Biyar na Kasar, inda ya ce matukar ba ta yi hakan ba nan da mako guda zai daukaka kara don neman diyyar ba ta masa suna da ta yi.
