Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ki amincewa da dokar da ta kafa jami’ar ilmi ta tarayya da ke Numan a Jihar Adamawa.

A wata wasikar kin amincewa da shugaban ya aikawa da shugaban majalisar wakilai Tajuddeen Abbas, wanda mataimakin shugaban majalisar wakilai Benjamin Kalu ya karanta wasiar a zaman majalisar na yau Talata.
Banjamin ya ce Wasikar ta bayyana cewa daga cikin dalilan shugaban na Kin amincewa da kafa Jami’ar sun hada da sashe na 22 na dokar da ya bayar da iko kan filin gwamnan jihar, maimakon shugaban Kasa kamar yadda doka ta tanada dangane da batun filayen jami’o’in gwamnatin tarayya.

Wasikar ta kuma bayyana cewa an cire batun bayar da digiri a cikin sashi na 25 (b) na dokar wadde ake son kafa jami’ar.

Acewar Wasikar shugaba Tinubu ya ce bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, na da damar kin yarjewa da kowacce doka da majalisa ta gabatar masa.
A shekarar 2024 da ta gabata ne Majalisar Wakilan ta gabatar da dokar, tare da amincewa da samar da jami’ar a Numan, tare da mikawa shugaba Tinubu bukatar don amincewa da dokar.
