Majalisar Wakilai ta Kasa ta amince da bukatar shugaban Kasa Bola Tinubu na kara kasafin kudin shekarar nan ta 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2.

Bukatar hakan na zuwa ne bayan karin kudaden shiga da aka samu daga wasu hukumomin gwamnatin Kasar.
Hukumomin da suka tara kudaden sun hada Hukumar Tara Haraji ta Kasa FIRS inda ta tara naira Tiriliyan 1.4, sai hukumar hana fasa kauri ta Kasa Kwastam Naira Tiriliyan 1.2, sannan wasu daga cikin hukumomin gwamnati naira Tirilyan 1.8.
A wani taron manema labarai da Kakakin Mataimakin majalisar Hon Philip Agbese yayi a yau Juma’a a Abuja, ya ce majalisar ta kuduri aniyar taimakawa shugaban Ƙasa wajen ganin an tabbatar da dimokuradiyya a Kasar.

Acewar Philip Majalisar ta yi na am da shawarar shugaban Tinubu na yin duba da kasafin kudin na 2025 don kara yawan kudaden zuwa Naira tiriliyan 54.2.

Philip ya ce matakin hakan na da kyau sosai domin hakan ya na nuna jajircewar gwamnatin tarayya na kara farfaɗo da tattalin arzikin Kasa da kuma inganta rayuwar ‘yan Kasar.
Bugu da kari ya ce za a mayar da hankali akan bangarori, musamman noma wanda zai taimaka matuka wajen kara wadatar abinci a Najeriya, inda aka shigar da kudaden cikin Bankin noma, inda shirin zai kara karfafa manoma da kuma kara inganta ci gaban karkara.
