Al’amarin ya faru a ranar Asabar a unguwar Tudun Yola a Kano.

Yayin da mu ka zanta da matashin angon ya shaidawa Matashiya TV cewar, amaryar tasa ta yi alƙawarin aurensa muddin ya iya ɗaga wani mungureren ƙarfe da hannu ɗaya sannan ya bata naira dubu ɗaya.


A wannan lokacin matashin ya yi ta maza ya daddage ya ɗaga ƙarfen, daga nan ne kuma su ka nufi hanya domin siyo biskit da alewa da nufin zuwa ƙofar gidansu matashiyar budurwa a shafa addu’a.
Bayan zuwa aka bayar da naira dubu guda a gaban wakilin da ta amince ya zama waliyyinta aka biya naira dubu lakadan tare da shafa addu’a.
A cewarsa, lokacin da su ke ƙulla wannan aure mahaifin amaryar na gefe yana saurarensu amma bai ce uffan a kai ba.
Zuwa yanzu matashin sun tsayar da ranar Laraba domin ci gaba da shagali tare da tafiya don dakko amarya.
Tuni iyayensa su ka ba da amanna tare da cewar ba zai saketa ba kuma za a basu amarya a ranar Laraba.
Da yake batu ne da ya shafi addini kuma a Kano, Matashiya TV ta ji daga bakin babban kwamandan Hisbah a Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya ce maslahar guda ce tak, matuƙar mahaifinta ya amince to fa aure ya ƙullu, amma muddin mahaifin bai amince ba, to batun ya zama shiririta.
Zuwa yanzu yan uwan ango na ta murna bisa samun amarya a ɓagas yayin da mahaifiyar amarya ta ce sam ba ta san zance ba.