Cutar murar tsuntsaye ta yi sanadiyyar mutuwar tsuntsaye 300 a jihar Filato.

Babban jami’in kula da dabbobi na jihar Dakta Shase’et Sipak ne ya bayyana haka yau Laraba a Jos babban birnin jihar.
Ya ce cibiyar bincike kan harkokin dabbobi ta ƙasa ce ta tabbatar da lamarin.

Gonar da lamarin ya shafa na a ƙaramar hukumar Bassa a jihar.

Bayan samun labarin faruwar barkewar cutar, sun yi gaggawar zuwa wajen tare da ɗaukar alamu na nau’in cutar kuma su ka tabbatar.
Tuni su ka ɗauki matakan kariya ciki har da karɓe ikon gonar na wani lokaci domin ɗaukar matakan da su ka dace.