Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun hallaka mutane hudu, tare da yin garkuwa da mutane da dama a wasu hare-hare da suka kai wasu yankuna a Jihar Zamfara.

Daga cikin wadanda ‘yan bindigan suka hallaka ciki harda yara biyu.

Mai sharhi kan sha’anin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zagazola Makama ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da y fitar a yau Talata.

Acewarsa ‘yan bindigan sun kai hare-haren ne daga ranar Lahadi zuwa jiya Litinin, a ƙananan hukumomin Gusau da Bukuyyum.

Makama ya ce a garin Shemori da ke cikin yankin Mada a Jihar, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mata shida da misalin karfe 8:30 na dare a ranar Lahadin da ta gabata.

Kazalika Makama ya kara da cewa da safiyar jiya Litinin, wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari garin Kairu da ke yankin Zugu, inda suka hallaka mutane biyu tare da yin garkuwa da mutane da dama.

Bugu da kari ‘yan bindigan sun kuma kai wani hari a Hayin Bajumi da ke cikin garin Mada a ƙaramar hukumar Gusau, inda suka cinna wuta a gidan wani mutum mai suna Aliyu Usman, wanda hakan yayi silar mutuwar ‘ya’yansa biyu, Ishaq Aliyu mai shekaru biyar da kuma Jafar Aliyu mai shekaru biyu.

Sannan maharan sun yi garkuwa da matar makwabcin Aliyu Usman tare da jaririnta mai shekara daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: