Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya musanta zargin da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya Sanata Nashata Akpoti-Uduagha ta yi masa na yunkurin yin lalata da ita.

Mai bai’wa Akpabio shawara kan harkokin yada labarai Kenny Okulogbo ya musanta zargin na Nashata, a yayin tattaunawarsa da Jaridar Punch a yau Juma’a.
Kenny ya bayyana cewa dukkan zarge-zargen da Sanatar ta Kogi ta yi akan Akpabio ba bu kamshin gaskiya a cikinsu, ta yi hakan ne sakamakon cire ta da aka yi daga shugabancin Kwamitin Majalisar ta Dattawa mai kula da harkokin albarkatun Kasa.

Acewarsa nan ba da jimawa ba shugaban Majalisar zai mayar da martani akan zargin na Nashata da kansa, tare da fitar da sanarwa a hukumance.

A wata hira da aka yi da Sanata Nashata a safiyar yau Juma’a, ta ce Akpabio ya nemi yin lalata da ita kafin amincewa da kudurorin ta da take gabatarwa da Majalisar.
