Jami’an Sojin Operation Fansar Yamma sun samu nasarar kama Shugaban ’yan Bindiga nan Kachallah Hassan Nabamamu da ke kai hare-hare a yankin Mada, Tsafe, da kuma wasu yankunan na Jihar Zamfara.

Jami’an sun samu nasarar ne a wasu hare-hare da suka kai Hegin Mahe, Ruwan Bore, Mada, da ke Ƙaramar Hukumar Gusau a jiya Alhamis.
Kafin kama hatsabibin dan bindigan jami’an sun yi musayar wuta, dashi inda suka hallaka wasu yaransa, inda hakan ya sanya shugaban ‘yan bindigar shige cikin wani gida, wanda hakan ya bai’wa jami’an sojin damar kamashi.


