Wasu Manoma Tara sun rasa rayukansu a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari Kauyen Karaga da ke yankin Bassa a cikin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Wasu Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun hari garin ne a cikin daren Laraba, inda suka farmaki mutane a gidajensu.
Bayan hallaka manoma tara ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa wasu mutane shida, tare da sace shanu da dama a yankin Farin-Doki da ke cikin karamar hukumar ta Shiroro a Jihar.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa bayan kai hari garin na Karaga, maharan sun zarce garin Farin-Doki, inda suka yi garkuwa da mutane shida, tare da shanu masu yawa.

Wata ta majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a Juwu-Farin-Doki da ke yankin Erena duk da cewa babu rahoton rasa rayuka .
Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Neja Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa zai yi karin haske akai, bayan samun cikakken rahoton harin,
