Tsohon mataimakin shugaban Kasa Alhaji Atiku Abubakar ya nuna takaicinsa bisa matsalar da kunno kai a Majlisar Dattawa tsakanin shugaban Majalisar Sanata Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti.

 

Atiku ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa lamarin abu ne mai tayar da hankali, inda ya bukaci da a gudnar da bincike mai zurfi akan batun, tare da bayyana mai gaskiya a tsakaninsu.

 

Acewar Atiku Majalisar ya zama wajibi shugabannnin majalisar su kasance masu gaskiya da amana, girmama ofisoshinsu da kuma ‘yan Kasar da suke wakilta.

 

Tsohon Mataimakin shugaban ya ce cin zarafin Mata ta hanyar neman yin lalata da su a guraren aikinsu, babban kalubale ne da ke hana samar da ci gaban Kasa.

 

Ya ce a don haka ba za a yi falali da batun ba, musamman idan sun shuafi jami’in gwamnati.
Alhaji Atiku ya bukaci da shugaba Bola Tinubu da ya sanya baki akan lamarin da ke faruwa Tsakanin Natasha da Akpabio.

Leave a Reply

%d bloggers like this: