Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da sansanonin rundunar soji a jihar Zamfara, musamman ga yankunan da su ke fama da matsalar rashin tsaro da harin ƴan ta’adda.

Buƙatar hakan ta taso ne bayan gabatar da wani ƙuduri a jiya Talata yayin zaman majalisar, daga ɗan majalisa Hassan Shinkafi mai wakiltar ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi a zauren majalisar.

Da ya ke gabatar da ƙudurin ɗan majalisar daga jam’iyyar PDP ya koka dangane da ta’azzarar rashin tsaro a ƙananan hukumomin Shinkafi da Zurmi, tare da cewa hare-haren su na zama sanadiyyar mutuwar mutane da kuma yin garkuwa da waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.

Hassan ya kuma ƙara da cewa majalisar tana sane da irin ƙoƙarin gwamnan jihar na tabbatar da tsaro a jihar, ciki kuwa har da ƙirƙiro ƙungiyar tsaro ta musamman a jihar.

Shinkafi ya bayyana cewa sama da ƙauyuka 40 ƴan ta’addar su ka mamaya, tare da tursasa al’ummar yankunan barin gidajensu gaba ɗaya.

Ya kuma nuna damuwarsa dangane da janyewar jami’an tsaron da aka tura yankunan a baya, inda su ka bar wajen bayan shafe makonni biyu kacal, wanda hakan ya bai’wa ƴan ta’addar damar dawo da hare-harensu.

Biyo bayan tabbatar da ƙudurin na sa majalisar wakilan ta buƙaci gwamnatin tarayya, da ta umarci rundunar sojojin ta samar da sansani na dindindin a yankunan da abin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: