Ministar masana’antu, kasuwanci da sanya hannun jari Dakta Jumoke Oduwale ta bayyana irin nasarorin da da Najeriya ta samu na samun sanya hannun jarin sama da Dala miliyan dubu 50, a matsayin irin alfanun da tafiye-tafiyen shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samar.

Ministar ta faɗi hakan ne jiya Talata yayin ganawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja, tare da cewa samun kashi 30 cikin 100 na ribar sanya hannayen jarin zai taimaka wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasar.

Ta kuma ce dole a lura da muhimmanci sanya hannayen jarin wanda tafiye-tafiyen shugaba Tinubu ya samar, ziyarce-ziyarcensa zuwa ƙasashen duniya ya haifar da ɗa mai ido.

Yayin da ta ke bayani game da ƙalubalen da ake fuskanta a ɓangaren sanya hannayen jari a duniya, ministar ta ce halartar taron ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arzikin da shugaba Tinubu ya yi samu ganawa da masu sanya hannun jari daga ƙasashen ƙetare, inda su ka yi aniyar sanya hannun jarin sama da Naira miliyan dubu 50 a Najeriya.

Ta kuma ce kamfanonin sun ziyarci ƙasa Najeriya don duba damarmaki, kuma sun ƙuduri aniyar tabbatar da sanya hannun jarin na su.

Jumoke ta kuma bayar da misali da kamfanin shigo da nama daga ƙasar Brazil, inda su ka ƙuduri aniyar sanya hannun jarin sama da Dala miliyan dubu biyu a Najeriya.

A ƙarshe ta ce ayyukan ma’aikatar ta su ne tabbatar da waɗannan ƙudure-ƙuderen zuwa na zahiri, tare da kawar da duk wani ƙalubale da zai hana tabbatuwarssu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: