Uwar gidan shugaban Kasa Bola Tinubu Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa nan bada jimawa Najeriya za ta gyaru daga halin da ta ke ciki.

Oluremi ta bayyana hakan ne a yayin buda baki da ta shirya a fadar shugaban Kasa da ke Abuja.

Uwar gidan ta Tinubu ta kuma jaddada muhimmancin jin-kai da tausayawa marasa karfi, inda ta bukaci da al’umma su kasance masu aikata alkhairi tsakaninsu da Allah ba tare da neman yabawa ba ko kuma amincewar mutane ba.

A ya yin Liyafar buda bakin Shugabar Sashin Nazarin Addini Musulunci ta Jami’ar Ilorin Farfesa Azeezat Adebayo ta ce tausayi da jin-kai babban a bu ne a tsakanin al’umma.

Acewar Azeezat wata Azumin Ramadan wata ne na koyon kyawawan halaye, tare da aikata alkhairi ga kowa, har ma da wanda ba musulmi ba.

Daga cikin wadanda suka halarci taron bua bakin sun hada da Uwagidan tsohon shugaban Kasa Dame Patience Jonathan, Matar mataimakin shugaban Kasa , Matan gwamnonin Jihohi, Ministoci Mata, Matan Ministoci, da kuma Matan shugabannin hukumomin Tsaro.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: