Tsohon Sanata a jihar Kaduna Sanata Shehu Sani ya ce jam’iyyar APC za ta cigaba da zama mai tasiri ko da cewar tsohon gwamnan ya fice daga cikinta.

Sanata Shehu Sani ya bayyana haka bayan da tsohon gwamnan jihar Malam Nasir Elrufai ya bayyana ficewarsa daga cikin jam’iyyar APC yayin da ya koma cikin jam’iyyar SDP.

A sanarwar da ya fitar, Shehu Sani ya ce komawar tsohon gwamnan Ramalan Yaro da manyan yan siyasa a Kaduna, zai ci gaba da haska ruhin jam’iyyar ko da cewar Elrufai ya fice daga cikinta.

Malam Nasir Elrufai dai ya bayyana dalilansa na ficewa daga cikin jam’iyyar wanda daga ciki har da yadda shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje ke jagorantar ta.

Tun a baya ake hasashen cewa Elrufai ya na shirin ficewa daga jam’iyyar, bayan zargin da aka yi kuka ya tabbatar da hakan a jiya Litinin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: