Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Ondo, Agboola Ajayi ya shigar gabanta yana mai kalubalantar nasarar gwamnan Luckyu Aiyedatiwa.

Alkalin kotun mai shari’a Lawal Garba ya bayyana cewa Ajayi ya shigar da karar ne bayan karewar wa’adin da doka ta tanada na shigar da karar.
Sannan Alkalin yakuma ce Ajayi bashi da hurumin da zai shigar da karar kan nasarar Lucky.

Kotun ta kuma ce karar ta shafi bangaaren cikin gida ne na jam’iyyar APC, ba hurumin wata jam’iyyar ba ne ta tsoma baki a ciki ba.

Tun dai a ranar 7 ga watan Yuni shekarar 2024 da ta gabata, Ajayi ya shigar da kara gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, inda ya kalubalanci takarar Aiyedatiwa sakamakon rashin cancantar mataimakinsa.
Inda bayan shigar da karagaban kotun babban Alkalin kotun ta Tarayya ya canza shari’ar zuwa kotun tarayya da ke garin Akure, a ranar 2 ga Disamba 2024, inda kotun ta yi watsi da karar tana mai cewa ba a shigar da ita akan tsarin doka ba.
Kotun ta kuma bayyana cewa lamarin ya fara ne tun a ranar 20 ga watan Mayu 2024 a lokacin da aka aikewa da hukumar INEC fom din takara, inda kuma masu shigar da kara suka shigar da kara kotu a ranar 7 ga Yuni 2024, bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da doka ta tanada.
Kotun ta ce hakan ya sanya ta yi watsi da karar tare da umartar Ajayi da ya biya Naira Miliyan 2 ga kowanne daga cikin wadanda yake kara.