Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya kaddamar da rabon tallafin azumin watan Ramadan ga ‘yan gudun hijira 77,000 da ke sansanoni daban-daban na Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya na mai cewa gwamnatin Jihar ta dauki matakin bai’wa ‘yan gundun hijirar tallafin ne, domin tallafawa wadanda suka rasa mutsugunnansu.
A yayin kaddamar da tallafin gwamnan ya bayyana cewa kowacce mace daya da ke cikin sansanin za ta samu turmin atamfa, da buhun shinkafa mai nauyin kilogram 10, da kuma kudi.

Sannan gwamna Ahmad ya bayyana cewa dukkan kuma wani magidanci da ke zaune a sansanin shima zai samu tallafin shadda da kudi.

Acewar sanarwar gwamnatin Jihar ta ce tallafin zai kawowa ‘yan gudun hijirar sauki wajen gudanar da bukukuwan Sallah karama da ke gabatowa.
Gwamnan ya kuma tabbatar da aniyarsa ta bin dukkan hanyoyin da suka kamata wajen ganin ‘yan gudun hijarar sun koma muhallansu.