Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya bayyana cewa, aikinsa shi ne hidimtawa al’ummar jihar da suka zaɓe shi ba wai yin cece-kuce da masu sukarsa ba.

Gwamnan ya ce a tsawon watanni 22 da ya shafe yana mulkin jihar, gwamnatinsa ta bunƙasa harkar noma da kiwo, ilimi da kuma samar da tsaro a jihar.
Ya yi wannan jawabin ne dai bayan kammala zaman buɗa bakin azumin Ramadan da wasu jagororin kafar sadarwa ta zamani, a gidan Sir Kashim Shettima a ƙarshen makon da ya gabata.

Uba Sani ya ce ya fi mayar da hankali kan ayyukansa kuma ba zai bari wani abu ya ɗauke masa hankali da yin rigima da kowa ba, ko kuma maganganu marasa kan gado da basu da wani amfani.

Gwamnan ya ƙara da cewa ƙarancin ruwan famfon da jihar ke fama da shi ya kusa zuwa ƙarshe nan ba da daɗewa ba, ruwan zai wadata kuma a duk faɗin jihar.
Ya kuma ce gwamnatinsa tuni ta warware matsalar biyan albashin ma’aikatar samar da ruwan sha ta jihar na Naira miliyan 800, da kuma biyan kudin wuta kimanin miliyan 1,300.
A ƙarshe ya yabawa masu amfanin da shafukan na sada zumunta wajen bayyana ayyukan gwamnatin, tare da alƙawarin basu dukkan gudunmawar da ta dace.